Shugaban kasar Faransa Macron ya ce kasarsa ta samu nasarar farko kan annobar cutar Korona duk da yake ba a kammala fafatawa ba duba da irin illar da cutar ta yiwa kasar.
Yayin da yake gabatar da jawabinsa zuwa al’ummar kasar, Macron ya ce yana farin cikin bisa nasarar da suka samu wanda zai bada damar bude harakokin kasuwanci da suka shafi shagunan sayar da abinci da wuraren shan kofi daga wannan litinin.