Wasu da ake zargin mayakan kungiyar IS ne a yammacin Afrika (ISWAP) a halin yanzu suna fafatawa da sojoji a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wasu fararen hula sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogayen ayarin motocin yaki, ta hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.
Fararen hula sun yi ikirarin cewa sun kai rahoton motsin ‘yan ta’addan ga jami’an tsaro amma ba a dauki wani mataki ba kafin wannan mummunar kungiyar ta afkawa garin Askira bayan sa’o’i kadan.
Yayin da yake tabbatar da hare-haren, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Engr Abdullahi Musa Askira, ya shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa a halin yanzu ‘yan ta’addan da sojoji suna musayar wuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi wa Dagaci Yankan Rago a zamfara
“Eh, a halin yanzu ISWAP na kai hari garin Askira. An sanar da ni cewa sojojinmu suna fada da su”
“Mutane na sun gaya mani cewa maharan sun zo ne da motoci kusan 16 kuma akwai rudani a duk fadin garin a yanzu,” inji Engr. Askira tace.
Wani jami’in civilian JTF, Yakubu Luka, ya ce nan take maharan suka far wa garin, inda suka Farmaki sansanin sojoji dake yankin.
“Muna sa ran samun tallafi daga al’ummar da ke kusa, yayin da nake magana da ku ana ci gaba da harba manyan bindigogi.”
“Muna kira ga hukumomi da su aika da jiragen yaki domin tallafawa sojojin kasa. Mun yi yawa; manyan motocin bindiga biyar ne kawai muke da su.” Yakubu yace.
Sai dai har kawo hada rahoton Babu cikakken labari kan asarar da Akayi sanadiyar wannan kazamin fadar da ya barki tsakanin bangarorin biyu.