Farashin ɗanyan Mai ya ragu da Dala ɗaya a kan kowace ganga a ranar Litinin 7 ga watan Satumba, wanda shi ne mafi muni tun rage farashin da ƙasar Saudiyya ta yi a watan Yulin bana.
Faɗuwar farashin ya zo ne lokacin da ƙasar Saudiyya ta yi ragin manta domin jigilarsa zuwa nahiyar Asiya, a cikin watanni biyar baya a lokacin da ake farfaɗowa daga buƙatar Man sakamakon ɓullar cutar Korona.
Ɗanyan mai samfurin Brent wanda a baya ake sayarwa a kan Dala 41.75 a kowacce ganga ya faɗi da kaso 91% kwatankwacin Dala ɗaya a dai-dai 12 na dare, bayan ya ragu da Dala 41.51, a watan Yuli.
https://dimokuradiyya.com.ng/korona-ta-kaskantar-da-farashin-danyen-man-amurka/
Saudiyya wacce ita ce kan gaba wajen fitar da ɗanyan mai a duniya ta bayyana ragin man nata ne na watan Oktoba mai kamawa a hukumance a kan ɗanyan mai samfurin Arab Light wanda ta ke sayarwa ga Nahiyar Asiya.
Ƙungiyar ƙasashe Masu Fitar da Man Fetur (OPEC) da takwarorinta sun sauƙaƙa dokar da suka yi ta rage yawan man da kowace kasa take haƙowa na ganga miliyan 7.7 a rana a watan Agusta bayan da aka fara farfaɗowa daga annobar Korona.