Hukumar sauraron kararrakin jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ta cimma yarjejeniya da kungiyar masu sarrafa shinkafa game da farashi.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin Gado ya shaida wa BBC cewa bayan sun tilasta wa ‘yan kasuwa sassauta farashin suga yanzu kuma sun waiwayi bangaren shinkafa.
Ya ce kungiyar masu sarrafa shinkafa ta jihar Kano RIFAN ta amince ta sassauto da farashi zuwa N15,500 ga ƴan kasuwa duk buhu 50KG, yayin da su kuma su sayar wa mutane kan farashin N16,000 duk buhu.
Ya ce ƙungiyar ta amince ta samar da tirela 30 duk mako domin al’ummar Kano, kuma mutum ba zai iya sayen sama da buhu biyu ba.
Ya ce hakan zai yi maganin masu ɓoye kaya da tsula wa kayayyaki farashi mai tsada.
-Bbc Hausa