By Ishaq Dabai
Hukumar dake kula da kididdigar farashin kayan masarufi a Nigeria, ta ce a watanni biyar da su gabata, hawan da farashin kayan masarufi yayi yayi kasa zuwa kaso 17.01 a watan Agusta, sabanin na watan Yuni da yake a 17.38.
Wani rahoto daga hukumar Kididdiga ta Nigeria (NBS) ta ce hukumar mai alhakin kula da farashin Masarufin ce ta sanar da hakan a safiyar ranar Laraba a Abuja.
Yanzu dai adadin 0.37 ne ya Ragu, kan yadda yake a da. Kuma tun a watan Maris ne dai halin farashin ya fara sauya salo.