Gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin farashin man fetur zuwa N143.80 a kan kowacce lita.
Hukumar ƙayyade Farashin Mai ta Kasa (PPPRA) ta bayyana haka a wata sanarwar da ta fitar a yau Laraba.
Sanarwar da aka raba wa dillalan mai dauke da kwanan watan daya ga watan Yuli ta ce, “Bayan la’akari da yanayin kasuwar mai a watan da ya gabata da kuma nazarin halin da dillalai suke ciki, muna bayar da shawarar a ƙara farashin mai zuwa tsakanin N140.80 da N143.80 daga farkon watan Yulin shekarar nan.
“Mun umarci dukkan dillalai da su sayar da mai a tsakanin waɗannan farashin kamar yadda PPPRA ta ba da shawara.
Kusan sau uku hukumar tana rage farashin man a bana sakamakon faɗuwarsa a kasuwar duniya, ko da yake wannan ne karon farko da aka ƙara kudinsa a shekarar nan da muke ciki.