Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta karyata ikirarin da Boko Haram suka yi cewa sune suka kakkabo jirgin saman sojin Nijeriya.
Rundunar sojin saman ta yi watsi da bidiyon da Boko Haram ta fitar wanda ta yi iƙirarin harbo jirgin rundunar sojin saman a jihar Borno arewa.
Rundunar dai ta ƙaryata Boko Haram ne a cikin sanarwar da kakakinta Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar, inda ya ce sanarwar bidiyon na Boko Haram ƙarya ce tsagwaronta, wanda suka hada domin yaɗa farfaganda.
Rundunar sojin ta ce tana tunanin jirgin ya yi hatsari ne.
Gankwet ya ce bacewar jirgin na ta mai kirar Alfa Jet (NAF 475) yana dauke da mutum biyu ne.
Bidiyon da Boko Haram ta fitar ya nuna mayaƙa ɗauke da makaman harbo jirgin sama da masu cin dogon zango, da kuma tarkace da gawar matuƙin jirgin. Rundunar sojin ta ce an tsayar da bidiyon aka haɗa yadda jirgin ya kama da wuta daga sama yayin da yake kokarin fadowa.
Rundunar ta ce ko da yake har yanzu tana kan nazari a kan bidiyon, amma a bayyane yake cewa yawancin sassan bidiyon an haɗa ne da gangan don yaɗa ƙaryar cewa an harbo jirgin.
Rundunar ta nemi ‘yan Nijeriya su yi watsi da bidiyon wanda ta kira shi da ‘farfagandar ƙarya da Boko Haram ta shirya’.