Shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya jinjinawa gwamnatin Tarayya da duk wadanda suka tallafa wajen ganin an bai wa Jami’ar lasisin fara karatu a Nijeriya.
Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya yi wannan yabon ne a ranar Laraba a sanarwar da ya fitar mai dauke da sa hannunsa kuma aka rabawa manema labarai.
Idan za a iya tunawa a ‘yan kwanakin nan ne gwamnatin tarayya ta bada lasisin fara aiki ga jami’o’i 20 masu zaman kansu ciki har da Jami’ar Maryam Abacha.
Farfesa Gwarzo ya ce bada lasisin ya sanya shi matukar farin ciki wanda wannan ya tabbatar da burinsa na ganin ‘yan Najeriya musamman matasa sun samu ilimi wanda za a kwatanta shi da irin na kasashen Turai wanda hakan zai sa su rika gogayya da sauran daliban jami’o’i a fadin duniya.
Farfesa Gwarzo har wala yau ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Majalisar zartarwa ta kasa, da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) da sauran masu fatan alkhairi wadanda suka kira shi da masu turo sakon taya murna bisa samun lasisin Jami’ar.
Farfesa Abubakar Gwarzo ya kara da cewa lasisin da gwamnatin tarayya ta bai wa Jami’ar zai bashi kwarin gwiwa wajen ci gaba da ayyukan ginin wasu tsangayoyi da sashin karatu a matsugunin jami’ar dake gari Gwarzo.
Ya bada tabbacin cewa, Jami’ar za ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da dalibai na kwarai. “abin farin cikinmu ne a ce mun ceto jihar Kano da Nijeriya da Afrika daga karancin jami’o’i”.