Majalisar Dattawa a ranar Talata ta tabbatar da Farfesa Mahmood Yakubu, a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC a karo na biyu. Majalisar ta tabbatar da sunansa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa da majalisar sunansa a karo na biyu domin tabbatarwa.
Tabbatar da shi hakan na nuni da cewa zai sake kwashe shekaru biyar domin gudanar da aikinsa a matsayin shugaban Hukumar.