A wani rahoto da kafar CNN ta fitar ya bayyana cewa wasu da ba a gano ko su wane ne ba sun harbe Bing Liu, wanda mataimakin farfesan bincike ne a Jami’ar Pittsburgh..
Kafin harbe Farfesa Bing Liu mai shekaru 37 da haihuwa, a karshen makon da ya gabata, Farfesan wanda dan asalinkasar China ne ya yi nisa a binciken da ya ke yi na gano makarin kwayoyin cutar Coronavirus.
CNN ta rawaito cewa, ‘yan sandan yankin Ross Township sun bayyana cewa an samu gawar Farfesa Bing ne a yashe a cikin gidansa a ranar Asabar din da ta gabata, dauke da harbin bindiga a kansa da kuma wuyansa.
Bincike ya nuna nau’in kisan da aka yi wa Bing kisan kai ne da ba shi da alaka da kasancewarsa dan China, a cewar ‘yan sandan.
Wani abokin aikin Farfesa Bing Liu ya bayyana shi a matsayin zakakurin mai bincike da tsangayar kimiyyar halittu ta jami’ar Pittsburgh ke alfahari da shi.
Hukumomi a tsangayar sun yi alwashin kammala wannan bincike da Farfesa Bing Liu ya fara da nufin karrama kwarewa da hazakarsa.
-Alummata