Daga: Abbas Yakubu Yaura
A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari na gudanar da taron gaggawa da hafsoshin tsaro da shugabannin jami’an tsaro da wasu ministoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Taron wanda ya zo ne a cikin sabbin ayyukan ta’addanci, ciki har da harin da aka kai a daren ranar Talata a cibiyar gidan gyaran hali da tarbiyya da ke Kuje, a Abuja, sakamakon abubuwan da suka faru a baya-bayan nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/nahcon-ta-tabbatar-da-rasuwar-mahajjaciyar-jihar-kaduna-a-kasa-mai-tsarki/
‘Yan ta’adda ne suka kai hari a Cibiyar Kula da gyaran hali da tarbiyya dake Kuje, inda suka kubutar da fursunoni sama da 800 da suka hada da ‘yan Boko Haram.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne kungiyar da ke yankin yammacin Afirka (ISWAP) ta dauki alhakin kai harin.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa taron yana samun halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).
Haka kuma akwai ministocin harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola; Harkokin ‘yan sanda Maigari Dingyadi; ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya.); da babban lauya kuma ministan shari’a, Abubakar Malami.
Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Sojoji Laftanar Janar Farouk Yahaya; da babban hafsan sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao suma sun halarci taron.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta DSS Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.
Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; shima ya halacci wajen taron.