Tsohon mai Tallafa wa Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan watoo Doyin Akupe ya buakci gwamnatin tarayya da ta bijiro da fasahar zamani wajen yaki da matsaloling tsaro da suka dabaibayi kasar nan.
Mista Okupe ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da tashar Talabijin na Channels cikin ta na Gari Ya Waye wato “Sunrise Daily” a turance.
Ya yi bayani kan cewa a zamanin su lokacin Goodluck Jonathan na mulkin kasar nan, ya yi amfani da wannan fasaha wajen yaki da matsalar tsaro ta inda aka yi ta bibiyar aikace-aikacen mayakan Boko Haram a garin Bama.
“Lokacin da muke kan karagar mulki akwai hare hare da yan boko Haram suka kai a garin Bama inda suka kone gidaje, to amma mun yi amfani da na’urar satetellite inda muke yi wa garin kallo har hanji, domin har muna iya kirga gidajen da aka kona da ma wadan da ba a kona ba” cewar Okupe.
Da yake tsokaci dangane da yadda gwamnatin tarayya ke yunkurin yaki da matsalar tsaro, Okupe ya ce matakin sulhu da yan ta’adda ba shi ne mafita ba domin babu abinda hakan zai haifar face kara ta’azzara matsalar.
Tsohon Babban Mai Tallafa wa Tsohon shugaban Kasar har wa yau ya kara da cewa babu wani alfanu kan baiwa yan ta’adda dama domin hakan na baiwa masu daukar nauyin su ne kafa ta kara taimaka musu.