Gwamnan Beirut, Marwan Abboud, a ranar Laraba ya bayyana cewa sakamakon fashewar nakiya a tashar saukar kayayyaki a birnin na Beirut, fiye da mutum dubu dari biyu suka rasa muhallansu bayan da fashewar nakiyar ya tarwatsa gidaje da daman gaske.
Abboud ya shaida kafar watsa labarai ta MTV News cewa; mutane akalla 200,000 zuwa 250,000 ne suka rasa gidajensu, sai dai ya ce hukumomi suna aiki tukuru wajen ganin sun samar wa da al’umma abinci, ruwa da kuma kayayyakin more rayuwa.
Abboud ya tabbatar da cewa rahoton tsaro a shekarar 2014 ya gargadi yiwuwar fashewar abu a birnin Beirut din na Lebanon, a sakamakon adana wadansu abubuwa masu fashewa da ba a yi da kyau ba.
Ya tabbatar da cewa akalla ma’aikatan kashe wuta 10 suka rasa ransu, a yayin da aka yi asarar dukiyar da ya kai Dala biliyan 3 zuwa 5, inda ya ce ma adadin na iya zarce hakan.
Firaministan kasar, Hassan Diab a ranar Talata ya bayyana abin da ya fashe ya kai nauyin tan 2,750 na sinadarin ‘ammonium nitrate’ da ake ci gaba da ajiyewa a ma’ajiyar tashar ajiye kaya na Beirut har na tsawon shekara shida ba tare da daukar matakan kariya ba.