An samu firgici a Unguwar Sanusi da ke Kaduna bayan da wata Tukunyar iskar gas ta fashe kuma ta kashe wani yaro dan shekara bakwai tare da raunata wasu 10 a yankin, inji rahoton Daily Trust.
An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na yammacin ranar Litinin a lokacin da wani mai gyaran iskar gas ke hada wata silinda a wani gida da ke kan titin Meyere.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa tara daga cikin wadanda abin ya shafa ‘ya’yan gida daya ne da kuma mahaifiyar yaron da ya rasu da kuma mai gyaran iskar gas.
An tattaro cewa yaran sun taru domin kallon yadda mai gyaran ke kokarin hada silinda bayan ya cika shi da Iskar Gas.
Sai dai har kawo hada rahoton Nan, Ba a bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.
Usman Bala wanda shi ne mahaifin daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya tabbatar wa jaridar Daily faruwar lamarin.
Comments 1