Hukumomin babban asibitin Kabba da ke jihar Kogi sun bayyana cewa an garzaya da mai gidan giyar, Mrs Omofemi Oyehunwa da wasu mutane goma da suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani jim kadan bayan fashewar wani abu.
Dr Ibrahim Sule, shugaban sashin X-ray na asibitin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yammacin ranar Litinin a Kabba.
Sai dai Dokta Sule ya kara da cewa sauran wadanda abin ya shafa sun samu magunguna kuma an sallame su, amma Mrs Oyehunwa na ci gaba da zama a asibiti domin ci gaba da gwaje-gwaje.
“Dole ne mu kai ta sashin X-ray domin yin gwaji don tabbatar da cewa babu wani bakon abu a jikinta.
“Ta fita daga sashin X-Ray, tana tafiya da kanta, wanda ke nuna cewa tana saurin murmurewa daga raunin da ta samu a gindinta”, in ji shi.
A halin da ake ciki, shugaban karamar hukumar Kabba/Bunu, Hon. Moses Olorunleke ya bayar da umarnin a rufe duk wuraren sayar da giya a Kabba da karfe 7 na dare.
Haka kuma, ya umurci ’yan kasuwa masu sana’ar babura da aka fi sani da Okada da su dakatar da ayyukansu da karfe 10 na dare, inda ya ce duk wanda ya saba wa wannan umarni za a hukunta shi.