An gurfamar da wadansu Malaman har su biyar dake koyarwa a Kwalejin Ilimi na Tai Solarin da ke a garin Omu-Ijebu a jihar Ogun. Sun gurfana a gaban kotun majistare da ke zamanta a Abeokuta bisa zarginsu da aikata fashi da makami, tayar da hankalin al’umma da kuma cin zarafi da dai sauran laifuka.
‘Yan sanda sun cafke Malaman ne da suka hada da: Bakare Labake, Daniel Aborishade, Odunsi Omobolaji, Seyi Akinola da Ember Oluwatobi, bayan da aka shigar da kara a kansu daga wasu ma’aikatan kwalejin.
A yayin da ake gabatar da su a gaban kotu, lauyan ‘yan sanda Adekunle Opayemi ya shaidawa kotu cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Yulin 2019, wadanda ake zargin sun fasa ofishin kididdigar kudade na Kwalejin, inda suka sace wasu takardun na kudaden da aka kashe masu muhimmanci.
Mista Opeyemi ya ci gaba da cewa, wadanda ake zargin sun wallafa wadannan takardu na yadda aka kashe wasu kudade a Kwalejin a shafukan yada zumunta na Facebook da sauran kafafe.
Haka kuma wadannan Malaman sun yi wa matar mataimakin shugaban kwalejin, Sainab Agboola, fashi ta hanyar karbe motar da ta ke ciki, wacce motar da kwalejin ta mallakawa mataimakin shugaban Kwalejin ne, kuma a motar akwai zunzurutun kudi Naira dubu dari da ashirin, wayarta ta hannu da kuma wasu abubuwa na ta.
Mai shari’a Bolanle Adebowale, a yayin yanke hukunci ta umurci da a ci gaba da tsare Malaman har zuwa lokacin da za ta samu shawara daga sashen lura da harkokin zartar da hukunci kan al’umma.
Mai shari’a Adebowale ta bayyana cewa wadanda ake zargin za su iya belin kansu akan Naira dubu biyar kowannensu tare da kawo wa kotu mutum bibbiyu wadanda za su tsaya musu.
An kuma dage sauraren karar zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba.