By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a ranar Juma’a ta tabbatar da cewa an kwato wasu kudade da ake zargin ‘yan fashi sun yi awon gaba da su a harin da suka kai ranar Alhamis a wasu rukunin bankunan Uromi.
Mista Phillip Ogbadu, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).
Ogbadu ya ce an gano kimanin Naira miliyan 37 da motoci biyar da ake zargin ‘yan fashin ne suka yi amfani da su a wani daji da aka yi watsi da su.
Ya yi nuni da cewa ana zargin barayin sun yi watsi da kudaden da motocin ne bayan da suka fahimci cewa ‘yan sanda na kan hanyarsu ta zuwa wurin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu ‘yan fashi da makami ne da yammacin ranar Alhamis suka kai wani harin da wasu mutane suka kira hadaka na fashi da makami a wasu bankunan kasuwanci a Uromi, karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta jihar Edo.
Rahotanni sun bayyana ayyukan a cewar wasu shaidun gani da ido sun kwashe sama da awanni biyu ana gudanar da aikin.
Kazalika mataimakin gwamnan jihar Edo, Phillip Shaibu a ranar Juma’a ya kai ziyarar tantancewar zuwa garin na Uromi.