Ministan Yada Labarai da Al’adu Alhaji Lai Muhammad ya ce abin kunya ne da tausayi a ce jam’iyyar PDP da ta mulki kasar nan shekara goma sha shida wai ha ta san Matsalar fashin daji da garkuwa da mutane batu ne na Jihohi ba.
Ministan yana wannan batu ne a yayin tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja game da zargin PDPn cewa an gaza yin abinda ya kamata dangane da wadannan matsaloli.
Idan jama’a ba su mance ba a ranar Lahadi ne Jam’iyyar PDP ta yi wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja inda ta nemi gwamnatin tarayya da ta hada hannu da ita don kawo karshen matsalar tsaro.
Lai Muhammad ya kalubalanci PDP da ta tunkari jihohi kan su yi duk mai yiwuwa na ganin an hukunta wadanda aka kama da hannu dumu-dumu a harkar garkuwa da mutane da kuma fashin daji.
Ya ce matsalar ta’addanci wanda ita ce kai tsaye ta shafi gwamnatin tarayya, an yi kokarin dakile shi tare da gurfanar da dubban yan Boko Haram da aka chafke a dajin Kainji.
Ya ce ko da yake Jam’iyyar ta PDP ta fara nesanta siyasa cikin harkokin tsaron, to amma babatun ta ya fara wuce gona da iri.