Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola a ranar Talata ya Ƙaddamar da hanya mai tsawon kilomita 1.06 da Gwamnatin Tarayya ta sake ginawa a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano dake Jahar Kano.
Fashola wanda ya samu wakilcin Kwanturolan Ayyuka na Ƙasa a Kano Yahaya Baba-Ali ta bayyana cewar aikin wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na gyara hanyoyi a Manyan Makarantun Ƙasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kilo ta janyo bau: An sace motar Dan jarida a sakariyar jam’iyar APC na jihar Kaduna
“Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta sanya a fara aikin, tare da tabbatar dacewa dukkanin ayyukan hanya an gudanar da su a makarantun Gwamnatin Tarayya a Faɗin Ƙasar,” inji shi.
Ministan a lokacin da yake jaddada ƙudirin sa akan wasu hanyoyi da suka Lalace da ake gyaran su a halin yanzu, ya baiwa Ƴan Najeriya ta tabbacin ganin an gudanar da kyakkyawan aiki, tare da samar da yanayin koyo mai kyau.
“Mun samu nasarar gyara hanyoyi na manyan Makarantu 46 a faɗin Ƙasar nan, mun miƙa 29 ya zuwa Shekarar 2021, kuma muna da ƙarin wasu 17 da za’a miƙa su.
“Ma’aikatar a halin yanzu tana aikin hanyoyi 30 a Manyan Makarantu daban-daban a faɗin Ƙasar, wanda yanzu adadin yakai hanyoyi 76.
A jawabinshi, Babban Likitan Asibitin Koyarwa na Aminu Kano Farfesa Abdulrahman Sheshe ya yabawa Gwamnatin Tarayya da irin waɗannan shirye-shiryen Tallafawa, inda yace zata taimaka matuƙa a harkokin Asibitin.