Akalla fasinjoji 20 ne aka ruwaito sun kone kurmus da wuta da ransu a ranar Juma’a sakamakon wani mummunan hatsari da ya afku a yankin Ibarapa na jihar Oyo.
DAILY POST ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Wani A Fadar Shugaban Kasa Na Goyon Bayan Atiku – Wike
Majiyoyi sun shaidawa Dimokuradiyya cewa hatsarin ya rutsa da motoci biyu, wata motar bas ta kasuwanci da kuma Sienna.
Hadarin ya afku ne a Lanlate Junction dake garin Maya a karamar hukumar Ibarapa ta Gabas na jihar Oyo.
Motocin biyu da aka ce suna tafiya ta bangarori daban-daban sun yi karo da juna inda wutar takama nan take.
Wata majiya ta ce fasinjoji biyu ne kawai suka tsira daga hatsarin yayin da wasu da dama da motocin suka kone kurmus ta yadda ba a iya gane su.
Shugaban karamar hukumar Ibarapa ta gabas Hon Gbenga Obalowo ya tabbatar da faruwar lamarin.
Obalowo, wanda ya jagoranci tawagar ceto zuwa wurin da hadarin ya afku ya bayyana abin a matsayin abin a matsayin abin tausayi matuka.
Ya yi amfani da damar wajen jajantawa iyalan wadanda suka mutu a lamarin.
Obalowo, yayin da yake magana ya kuma kara da cewa a halin yanzu mutanen biyu da suka tsira suna samun kulawa a asibitin Awojobi da ke Eruwa.
Ya ce an ajiye gawarwakin wadanda suka kone a dakin ajiyar gawa dake Asiitin.
Ya kuma yi kira ga masu ababen hawa, musamman direbobin ‘yan kasuwa da su yi taka-tsan-tsan a lokacin da suke kan mota.
A WANI LABARIN KUMA: Shugabancin Kasa 2023: Ina Fatan Tinubu, Ko Obi Ya Yi Nasara – Gwamna
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya mayar da martani ga takarar shugaban kasa na dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, inda ya ce burinsa ya sanya yankin kudu maso gabas ya zama jigon siyasa.
Umahi, wanda ya je fadar shugaban kasa ta Villa, a Abuja, domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin yi masa bayani kan kammala ginin wani sabon masaukin Gwamnoni a Asokoro, bai fito fili ya goyi bayan dan takarar jam’iyyar Labour ba, amma ya lura cewa muradin Obi na Shugabancin kasar na da kyau ga yankin.