A wani lamari na alamar hadin kai da zaman lafiya a tsakanin Kirista da Musulmi a Jihar Kaduna, a ranar Asabar sama da Fastoci 30 ne suka halarci wurin bikin Mauludin Annabi Muhammad S.A.W na bana.
Fasto Yohana Buru, babban mai kula da ma’aikatar bishara ta Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, wanda ya jagoranci fastoci sama da 30 da kuma manyan baki zuwa wurin taron da aka gudanar a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar PDP Ta Bayyana Ranar Da Zata Kaddamar Da Yakin Neman Zaben Ta
“Ya ce bikin Mauludi ya ba da dama ga Kiristoci su hadu don yin mu’amala, tattaunawa, da musayar saƙon fatan alheri da ƴan’uwansu musulmi domin samar da zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar.”
Buru ya taya Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad da Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Ibrahim Yakubu Elzazzaky, da Khalifa Sunusi Lamido Sanusi shugaban darikar Tijjaniyya murna, ya kuma shaida musu cewa, suna cikin filin wasan ne domin suma su kara karfafa kyakkyawar alakar dake tsakanin mabiya addinan biyu masu rinjaye (Musulunci da Kiristanci).
A cewarsa, su (Fastocin Kirista) suna son samar da ingantattun hanyoyi na inganta zaman lafiya da kuma juriya na addini a tsakanin mabiya addinai daban-daban.
“Dole ne mu tuna cewa Allah ɗaya ne ya halicce mu, kuma mu ’ya’yan Adamu ne da Hauwa’u, kuma dukanmu muna da littattafanmu masu tsarki (Littafi Mai Tsarki na Bible da Al-Qur’ani) daga Allah ɗaya wanda ya yi mana ja-gora a kan yadda za mu rayu cikin aminci da da juna.” Yace
Ya yi kira ga Musulmi da Kirista da su fara gudanar da addu’o’i ga al’ummar kasar nan ba tare da tsagaitawa ba tare da yin addu’o’i na musamman ga daukacin jami’an tsaron Najeriya domin samun nasarar gudanar da ayyuka a fadin kasar.
Tun da farko, daya daga cikin malaman addinin Musulunci Sheikh Tukur Abdulsalam, jami’in hulda da jama’a na kungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya, ya jaddada bukatar fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan biyu, inda ya yi kira ga musulmi da kiristoci da su rungumi al’adun gargajiya.
Yayin da ya yabawa Fasto Buru da tawagarsa da suka ziyarce su tare da hada kai da su wajen gudanar da bikin shekara-shekara, ya ce a shekarar da ta gabata ma dai sun halarci majami’ar sa domin murnar zagayowar haihuwar Yesu Almasihu.
Wakilan Musulmi daga Jamhuriyar Nijar, da Cameron, da Chadi, da Senegal, da Ghana, da Sudan, da Jamhuriyar Benin sun halarci taron Mauludin na bana a Kaduna.
A wani labarin kuma, Tsohon Shugaban PDP, Da Ya Ce Jam’iyyar Za Tayi Mulkin Shekaru 40 Ya Mutu
Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Vincent Ogbulafor ya mutu.
Ya rasu ne sakamakon matsalolin da suka shafi koda a wani asibiti a kasar Canada.