Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima ya kai ziyarar tuntuba a Kano da nufin tattaunawa da manyan jahohin kasar nan kan ayyukan da ke ci gaba da gudana a arewacin kasar gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Yayin da Kashim Shettima ya kai ziyara Kano tare da gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun ziyarci Aminu Alhassan Dantata, wani dattijon jiha kuma fitaccen dan kasuwa wanda ya bayyanawa dan takarar mataimakin shugaban kasa da mukarrabansa cewa ya daina jin dadin rayuwa kuma yana fatan barin wannan duniya cikin aminci.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kakkakin Majalissar Wakilai Ya Yaudare Mu — ASUU Ta Caccaki Gbajabiamila
Dantata mai shekaru 91, ya bayyana cewa ya zagaya duk jihohin Najeriya kuma ya samu abokai da dama tun yana matashi amma ya kasa tantance guda 10 da ke raye.
Ya kara da cewa “A gaskiya, ni kadai ne na rage a cikin iyalina tare da jikoki.”
Dantata ya bukaci duk wanda ya bata masa rai a sane ko kuma ya samu wuri a cikin zuciyarsa su yafe masa kamar yadda ya yafewa duk wadanda suka bata masa rai.
Dattijon ya bayyana matukar godiyarsa ga Kashim Shettima bisa wannan ziyara da ya kai masa, ya kuma yi addu’ar Allah ya kara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Ya kara da cewa “Allah kada ya barmu da kokarinmu, muna addu’ar Allah ya ci gaba da yi masa jagora da kariyarsa.”
Sauran ‘yan tawagar sun hada da Musa Gwadabe, Janar Lawal Jafaru Isah da Tanko Yakasai.
PRIME TIME NEWS ta rahoto cewa, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ziyarci aikin da ake yi na cibiyar cutar daji ta Kano wanda ke daf da kammalawa kafin ya tashi zuwa filin jirgin sama.
A wani labarin kuma, Wata Mata Ta Haihu Lokaci Kaɗan Bayan Likita Yace Ɗan Dake Cikinta Bashi Da Rai
Wata Mata mai suna Hannan Cole, cikin abin ban mamaki, Allah ya albarkace ta da samun karuwar haihuwar ɗa namiji bayan kammala bikin Kirsimiti.
Rahoto da muka samu daga Mail Online shine, an sanar da Hanna a dai dai lokacin da take kan gaɓar haihuwa cewar jaririn dake cikinta ya mutu a cikin mahaifarta sakamakon likitan baiji bugun zuciyar jaririnba.
Duk da abinda likitan ya faɗa mata amma bata yadda ba, sai da ta nemi likitan da ya sake yi mata hoton cikin nata saboda tana ji a jikinta cewar jaririn dake cikin nata bai mutu ba.