Dr Kayode Fayemi, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ya kai ziyarar yini daya ga Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra a Awka babban birnin jihar tare da maraba da shi a hukumance zuwa cikin kungiyar gwamnoni ta NGF.
Fayemi, wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Ekiti, ya bayyana Soludo a matsayin wani “kadara mai kima” a yayin ziyarar yayin da ya yaba masa kan kyawawan matakan da ya dauka kawo yanzu a kan karagar mulki.
Ya ce ya dade yana bibiyar al’amura a Anambra karkashin Soludo masu ban sha’awa, inda ya ce jihar ta yi sa’ar samun gwamnoni masu don samar da ci gaba.
Shugaban kungiyar ta NGF ya ce Soludo wani kari ne a cikin dogon jerin sunayen.
Da yake mayar da martani, Soludo ya yi maraba da Fayemi wanda ya bayyana a matsayin aboki na dogon lokaci tare da gode masa bisa wannan ziyarar da ba kasafai ba.
Farfesan a fannin tattalin arziki ya ce akwai bukatar masu ra’ayin ci gaba su kafa hadin gwiwa don ciyar da kasar nan gaba tare da mai da hankali kan ci gaban al’umma.
Ya yabawa shugaban NGF bisa halayensa na jagoranci tare da yin kira da a hada kai da juna wajen gina kasa.