By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) tace an samu rahoton hadurran ababen hawa 850 a babban birnin tarayya Abuja wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 159 da jikkata 1,572 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba.
Kwamandan sashin, RS7.1 na Babban Birnin Tarayya (FCT), Mista Oga Ochi, ne ya bayyana hakan a taron bita na musamman na shekarar 2021 da aka gudanar a Abuja.
Taken taron shi ne, “Sa kai daya wuce watannin Ember: kan rawar da jami’ai na musamman ke takawa wajen yakar hadurran ababen hawa.”
Ochi ya bayyana cewa wuce iyaka yana matsayin daya daga cikin manyan kalubalen dake fuskantar wadanda suke amfani da tituna a cikin babban birnin tarayya Abuja sakamakon wasu kyawawan hanyoyi a cikin yankin.
Sannan yace masu amfani da hanyar sukan yi amfani da kyawawan tituna kuma suna gudun ‘ wuce gona da iri, ya kara da cewa kashi 75 cikin 100 na hadurran na faruwa ne sakamakon wuce gona da iri.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Tsakanin Janairu zuwa 19 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, jimillar hadurran ababen hawa 850 (RTC) ne aka tattara a babban birnin tarayya Abuja wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 159 da jikkatar 1572.
A cewarsa, sun yi tasiri a ayyukan gudanar da sintiri, wayar da kan jama’a, samarwa da gyara ofisoshi, ayyukan ceto, shiga aikin bincike, kula da ababen hawa, gudanar da tarukan jama’a, da ziyartar majami’u da masallatai da dai sauransu.