By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Litinin ne mahukuntan birnin tarayya Abuja suka fara aiwatar da dokar hana shiga Sakatariyar Garki Area 11.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, da misalin karfe 7:00 na safe, anga jami’an tsaro a kofar shiga sakatariyar.
Wakilin NAN daya sa ido kan aikin tabbatar da tsaro ya lura cewa an mayar da ma’aikata da maziyarta da dama.
An ga wasu a kofar shiga suna gunaguni da rokon abasu damar shiga.
Da take yiwa manema labarai jawabi, babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da tabbatar da tsaro ga ministar babban birnin tarayya Abuja, Ikharo Attah, ta ce za a ci gaba da aiwatar da aikin domin tabbatar da bin doka da oda.
Ta ce babu gudu babu ja da baya kan aiwatar da wannan umarni, inda ta ce ba za a karbi hotunan katunan allurar a waya da kwafi ba.
Attah ta ce an baza tawagar jami’an tsaro a harabar hukumar ta FCTA da sakatarori da ma’aikatu domin sanya ido kan yadda ake bin doka da oda.
Ya ce, “Za mu bi diddigin hakan da gaske, mun kuma gargadi mutane da kada su dauki katinsu a waya, saboda muna son ganin katinsu na asali, kar a nuna mana katin riga-kafi a wayar.
“Za mu nemi katunan shaida kuma za mu daidaita katunan tare da katin rigakafin COVID-19 don kada ku kawo katin wani a matsayin na ku.”
Jaridar Dimokuradiyya ta cewa rundunar ta zagaya wasu daga cikin hukumomin FCTA da suka hada da, Hukumar Kare Muhalli ta Abuja, Sakatariyar Cigaban Jama’a da Hukumar Ilimin bai daya ta FCT.
Sauran Sun Hada Da Hukumar Ruwa Ta FCT, Hukumar Ilimi Ta Sakandare, Hukumar Kula Da Lafiya Matakin Farko ta FCT, Ma’aikatar Kiwon Lafiyar Jama’a, Hukumar Samar Da Ruwan Sha Da Tsaftar Muhalli Da Hukumar Fansho Ta Ma’aikatan Karamar Hukumar FCT.
Hukumar FCTA a ranar Talata, 11 ga watan Janairu, ta ce za ta hana ma’aikata shiga ofisoshinsu daga ranar 17 ga Janairu idan ba za su iya nuna shaidar rigakafinsu na cutar COVID-19 ba.
Babban mataimaki na musamman ga ministan babban birnin tarayya Abuja kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa Malam Abubakar Sani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Sani ya bayyana cewa wannan gargadin yana kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun babban sakatare na FCTA, Olusade Adesola.