By Ishaq Dabai
Majalisar zartarwa ta tarayya FEC ta amince da naira biliyan 38.4 don kammala wasu ayyukan hanyoyi da aka gada a jihohi biyar na tarayya kasar nan.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Mista Babatunde Fashola ne ya bayyana haka lokacin da yake yiwa manema labarai na fadar gwamnati tarayya jawabi a karshen zaman majalisar, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba a Abuja.
A cewarsa, jihohin da ke cin gajiyar aikin sune Benue, Bayelsa, Anambra, Imo da Nasarawa, inda ya kara da cewa dukkan ayyukan da abin ya shafa gadar su sukayi daga gwamnatocin baya.
Shima da yake nasa jawabin ga manema labarai kan sakamakon taron, Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu ya bayyana cewa Majalisar ta amince da Naira miliyan 10.7 a matsayin kari don kammala aikin noman rani na Rima a jihar Sokoto.
“Ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya ta gabatar da wata sanarwa ga majalisar don sake duba jimlar kudin kashi na biyu na aikin ban ruwa na kwarin tsakiyar kogi,“ Wannan shine kammala aikin ban ruwa na tsakiyar Rima a Goronyo, jihar Sokoto.
“Gwamnatin soja ta fara wannan kwangilar a shekarar 1999 sannan, an kammala kashi na farko, wanda ya kunshi hekta 873.
“Don haka, wannan bayanin yana neman a sake duba farashin aikin, tare da kara kusan miliyan 10.7 don mu sami damar kammala aikin, da fatan kafin karewar wannan gwamnatin a 2023,” in ji shi.
Ministan ya ce daga cikin burin gwamnati na kammala ayyukan 116 da aka gada, 34 sun kammala.