Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta amince da Kwantiragin kuɗi har Naira biliyan 64,686536,230 domin gina hanyoyi da gadoji a sassa daban-daban na Kasar, ciki har da Babban birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari a shirye yake domin cigaban Najeriya — Cewar Osinbajo
Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan Kafafen Yaɗa Labaru Garba da Ministan Babban Birnin Tarayya Malam Muhammad Musa Bello suka sanar da hakan a ranar Laraba, a lokacin da suke jawabi a ranar Laraba ga Manema Labaru, bayan kammala taron Muƙarabban Gwamnati a Fadar Shugaban Ƙasa dake Villa, Abuja.
Shehi Wanda yayi jawabi a madadin Ministan Ayyuka da Gidaje,Babatunda Fashola, ya bayyana cewar Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da yin ayyuka guda 15, da hanyoyi, da gadoji, kamar yadda Ma’aikatar ta buƙata.
Yace ” ɗaya an bada kwangilar domin gina hanya kashi na biyu zuwa Ikot-Ekpene-Aba zuwa Owerri kuma zai kama Naira biliyan N40,157,000,000 daza’a kammala cikin watanni 30.