Babban mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan yada labarai Femi Adesina ya bayyana cewa Najeriya na bukatar Shugaba mai takalmin karfe irin mai gidansa shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Adesina ya ce shugaba irin Buhari ne kaɗai zai iya maganin kowa musamman masu mugun nufi wa kasarnan.
“Cikin rubutu zube da yake fitarwa mako-mako, Adesina ya ce bai san dalilin da ya sa ya ji a zuciyarsa yana son shugaba Buhari ba, inda ya ce kalaman Shugaban Kasar na cewa zai yi maganin yan tada kayar baya kamar yadda aka yi a yakin basas yana kan turba.