Jerin sunayen mutanen da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo da ake yadawa don karramawa ta kasa, karya ne, a cewar gwamnatin tarayya.
Marigayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, da wasu sunayen mutane 436 sun shiga jerin a yanar gizo a karshen mako.
Haka kuma a cikin jerin sunayen akwai mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, magatakardar hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, Ishaq Oloyede, da kuma babbar daraktar kungiyar cinikayya ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala.
Ana sa ran za a gudanar da binciken ne a ranar 11 ga watan Oktoba a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sai dai a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnatin Tarayya Julie Jacobs ta fitar, ta ce gaskiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR, zai karrama ‘yan Nijeriya da suka cancanta da abokan Nijeriya, amma kuma a cikin jerin sahihancin. Har yanzu ba a bayyana sunayen wadanda aka zaba ga jama’a ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An jawo hankalin ma’aikatar ayyuka na musamman da ma’aikatun gwamnatin tarayya kan jerin sunayen wadanda wasu kungiyoyin kafafen yada labarai na yanar gizo ke yadawa da ake zargin an nada domin karramawa ta kasa.
“Duk da cewa gaskiya ne cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR, zai ba da lambar yabo ta kasa kan wadanda suka cancanta da abokan Najeriya a ranar 11 ga Oktoba, 2022, har yanzu ba a fitar da sahihan jerin sunayen wadanda aka zaba ga jama’a ba. Ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatocin tarayya za ta buga jerin sunayen a lokaci da daban.
“An umurci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da ake yadawa saboda yunƙuri ne na ‘yan jarida masu kishin ƙasa waɗanda manufarsu ita ce ta watsa labarai ko da irin wannan labaran na bogi ne.”
A wani labarin kuma: Jam’iyyar Labour Za Ta Kawo Karshen Rashin Tsaro Idan Aka Zabe Ta – Datti Baba-Ahmed
Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce jam’iyyarsa za ta kawo karshen kalubalen tsaron da ke addabar Najeriya idan har aka zabe ta karbi ragamar shugabancin kasar a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun 2023.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Ya yi wannan alkawarin ne a wata tattaunawa da wasu zababbun ‘yan jarida a Sokoto inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar Labour za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.