Daga: Abbas Yakubu Yaura
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige, a ranar Litinin, ya ce gwamnatin tarayya ba ta maka kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, a kotu ba, dangane da yajin aikin da kungiyar ta dade tana yi.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Ministan Kwadago Chris Ngige ya bayyana hakan, yana mai cewa ya yi nadama kan yadda shugabannin ASUU ba su ma fahimci shigo da yarjejeniyar hadin gwiwa ba, tsakaninsu da gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Masu Neman Takara A APC Kaduna Sun Janye Kararrakin Da Suka Shigar Kotu
Sanata Ngige a cikin wata sanarwa da shugaban hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago ta tarayya Olajide Oshundun, ya fitar, ya ce babban mataki da zasu iya dauka shine bayyana gaban kotun ma’aikata, don tayi musu alkalanci kan dogon yajin aikin da suka shiga.
Tsawon watanni bakwai ana tattaunawa da kungiyar, amma har yanzu abin da ya ci tura.
Ministan ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wajen taro na kungiyar NLC, wanda ya mayar da hankali wajen tarihin gwagwarmayar rayuwa da kuma aiki.
Akwai dokoki da ke jagorantar yajin aikin, Akwai ka’idojin ILO kan ‘yancin yajin aiki.
Babu wanda zai iya dauke shi. Ngige ya tuna cewa ya sasanta rikicin har sau biyu, na farko a ranar 22 ga watan Fabrairu, mako guda da fara yajin aikin da aka cimma, kuma ya dawo da kowa da kowa a ranar 1 ga Maris.
A cewarsa, abin da ya rage shi ne komawa ma’aikatar ilimi ta tarayya don sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2013.
Ngige, ya ce watsa ba yana nufin ba za a iya warware batun ba a gaban kotu.
Ya ce ko wanne daga cikin bangarorin da abin ya shafa, ma’aikatar ilimi ta tarayya da kuma ASUU za su iya tuntubar hukumar NICN domin sasantawa a wajen kotu. Ya ci gaba da cewa dole ne Najeriya ta kasance a karkashin doka kuma kada kowa ya yi amfani da rigimar don cin zarafin kowa.
A wani labarin kuma, ‘Yan bindiga Sun Kashe 4, Sun Sace 8, Tare Da Jikka Wasu Da Dama A Neja
Mutane hudu ne suka mutu sakamakon wani hari da wasu mmutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai a kauyen Fapo da ke karamar hukumar Lapai a jihar Neja.
An kuma ruwaito cewa mutane 8 sun samu munanan raunuka a daidai lokacin da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da 15 a harin da aka kai da sanyin safiyar ranar Litinin a kauyen.