Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a ranar Talata ta amince tare da daukaka Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso zuwa Jami’ar Ilimi.
Sakataren zartarwa na hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, a lokacin da yake mika lasisin aiki ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a Abuja, ya ce jami’ar an amince da ita a matsayin jami’a ta 61 a fadin kasar nan. SOLACEBASE ta rawaito.
KU KARANTA: Kano: Da Yawan Yan Kasuwa Da Masu Shaguna Sun Bujirewa Karbar Tsohon Kudi
Farfesa Rasheed ya yi alkawarin bayar da goyon bayan hukumar ga jami’ar a fannin ba da shawarwarin fasaha don samun ci gaba mai dorewa.
A halin da ake ciki, Gwamna Abdullahi Ganduje, yayin da yake karbar wasikar ya bayyana cewa, akwai bukatar a samar da sabuwar jami’ar saboda tarin masu son yin karatu a jihar.
Gwamna Ganduje ya kuma nuna damuwarsa kan rashin aikin yi da masu digiri na biyu ke fama da su, wanda ya sa gwamnatin jihar ta kafa wata cibiya ta bunkasa sana’o’i ta biliyoyin nairori mai suna Aliko Dangote kuma ta kaddamar da aikin horar da matasa makonni biyu da suka gabata.
Ya kara da cewa gwamnati ta kuma bullo da ilimin firamare da sakandare kyauta amma ya jaddada cewa hakan bai wadatar ba wajen biyan bukatun al’ummarta na ilimi.
Don haka ya ce sabuwar jami’ar za ta sanya ta zama jami’a ta uku a jihar da ke fuskantar matsin lamba a harkar ilimi, duba da yawan yan jihar.
A wani labarin kuma: Zanga-zanga Ta Barke A Ogun Kan Karancin Sabbin Takardun Naira
A ranar Talatar nan al’amuran kasuwanci sun durkushe yayin da wasu fusatattun mazauna jihar Ogun, suka fito domin nuna rashin amincewarsu da karancin sabbin kudin naira N200, N500, da N1000.
An gudanar da zanga-zangar ne a Sango-Ota, dake karamar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun.