Gwamnatin tarayya ta amince da zunzurutun kudade kimanin biliyan 6.25 don fara kiwon shanu a Jahar Katsina.Kamar yadda Jaridar Thisday ta wallafa a shafinta
Mai magana da yawun shugaban Kasa Muhammadu Buhari Garba Shehu yake bayyana haka a jiya, inda yake cewa an baiwa gwamnatin Jahar Katsina miliyan biyar don fara aikin kiwon shanu a Jahar.
Gwamnan Jahar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana haka shima a garin Dutsinma dake Jahar Katsina a jiya, inda yake cewa jahar zata jagoranci samar da wuraren kiwo.
Asibitin Usman Danfodiyo ya dakatar da ma’aikaciyar da ta caccaka wa jaririya allura
Yayi wannan bayani lokacin da yaje wajan taron kaddamar da cibiyar ruwa data share shekaru 29 a ginawa, wanda aka fara aikin tun 1992.
Gwamnan ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan irin yadda yake kawoma al’umma cigaba iri daban-daban, inda ya amicema Jahar Katsina da naira miliyan biyar don fara kiwon shanu.
A cewar sa ” shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amicema Jahar Katsina da naira biliyan 6.42 wanda daga ciki ne miliyan biyar suka fara isowa.”
“Nan da dan lokaci kadan zamu kira kamfanoni da za su fara gina wajajan da aikin zai fara.”
Aminu Bello Masari yace hakika gwamnatin tarayya na iya kokarin ta na ciyar da mahaifar shugaban Kasa gaba.
Gwmnan ya kuma yaba ma shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kokarin sa na kammala cibiyar samar da ruwa, sannan da titin Tsaskiya mai kimanin tsawon kilomita hamsin har zuwa Dutsinma.
Comments 1