Gwamnatin tarayya ta bukaci Jami’an kiwon lafiya na cikin alumma da su kasance cikin shiri don tunkarar cutar kyandar biri a kauyuka, da zarar da bulla.
Karamin ministan lafiya na tarayya Barrister Ekumankama ne ya bayar da wannan umarnin ga jami’an daidai lokacin da annobar ke ci yaduwa a tsakanin alumma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Osun: Oyetola Ya Shigar Da Kara Don Kalubalantar Nasarar Adeleke
Da yake jawabi a yayin bikin yaye jami’an kiwon lafiyan su kimanin 477 da ya gudana a Abuja, ya ce duba da yadda ake ci gaba da samun barkewar annoba, akwai bukatar ma’aikatar lafiya da sauran jami’an ta su kasance cikin shiri don samun nasarar dakile baki daya cutukan da ka iya bulla.
Ya kara da cewa jami’an kiwon lafiya dake gudanar da aikinsu cikin alumma, sune matakin farko wajen dakile duk wata annoba daka iya bullowa, da kuma tabbatar da yakar annobar bayan samun rahoton bullarta.
Ya shawarci alumma kan su ci gaba da bayar da rahoton bullar duk wata bakuwar cuta da suka gani, ga jami’an lafiya mafiya kusa da su.
A wani labarin kuma, Akalla mutane biyar ne suka mutu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani kamfani mai suna Royal West Africa Ceramics da ke Ajaokuta a ranar Juma’a.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce an kai harin ne da misalin karfe 8 na dare.
An ce wani dan kasar Indiya daya da sufeto ‘yan sanda biyu da direbobin kamfanin biyu sun mutu a harin.
Rundunar ‘yan sandan ta ce sufetocin sun mutu ne “a musayar wuta da ‘yan bindigar, kafin daga bisani kwamandan yankin da rundunar soji da ke yankin suka tafi zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma maharan sun gudu.
“kwamishinan yan sanda ya tabbatar da cewa rundunar ta himmatu wajen yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro da kuma masu ruwa da tsaki na kishin kasa domin ganin jihar ta kasance wuri mai aminci da tsaro ga kowa da kowa.
“Ya kuma umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID) da ya fara gudanar da bincike kan wannan mummunan lamari domin bankado musabbabin faruwar lamarin nan take da nufin gurfanar da wadanda suka aikata laifin. ”
A watan da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sanda uku da ‘yan banga biyar a wani harin kwantan bauna da suka kai a yankin Ajaokuta, lamarin da ya sa Gwamna Yahaya Bello ya dakatar da wani basaraken gargajiya tare da yi wa shugaban siyasar gundumar tambayoyi.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin amma jihar ta Kogi ta fuskanci tashe-tashen hankula a ‘yan watannin nan.
A cikin watan Yuni ne mayakan jihadi na yankin yammacin Afirka (ISWAP) da ke aiki a wajen sansanin da suka saba yi a yankin arewa maso gabas, sun kai harin bam a ofishin ‘yan sanda da ke gundumar Okehi ta Kogi, inda suka kashe dan sanda tare da rusa ginin.
A watan Afrilu, an kashe ‘yan sanda uku a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda a garin Adavi.
Dukkan hare-haren biyu dai kungiyar ISWAP ce da ta balle daga Boko Haram a shekarar 2016 ta zama babbar kungiyar masu jihadi a yankin.
Kungiyar ce ta dauki alhakin fasa gidan yarin na baya-bayan nan a wajen Abuja babban birnin Najeriya, inda aka sako daruruwan fursunonin da suka hada da kwamandojin jihadinta 64.