Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin kula da muhalli ta bada kwangilar gina gada, da gyara matsalar zaizayar kasa da kuma shawo kan ambaliyar ruwa a fadin kogin Kaduna domin hade kananan hukumomin Zango Kataf da Kauru dake jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, a lokacin da yake mika takardun kwangilar ga kamfanin kwangila a Kaduna, ya kalubalanci dan kwangilar da ya bi yarjejeniyar da aka amince da ita.
Injiniya Anthony Dasibo Uruaka wanda ma’aikacin ofishin kula da muhalli ne, SGF ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya na samar da ababen more rayuwa ga jama’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Zai Raya Najeriya Kamar Yadda Ya Raya Legas Idan Yayi Nasara – Okiro
A nasa jawabin jagoran aikin wanda kuma mamba ne mai wakiltar mazabar Zango Kataf da Jaba a majalisar wakilai ta kasa Amos Gwamna Magaji ya ce idan aka kammala aikin gadar za ta zama hanya mafi sauri da zata sada mutum daga Zango Kataf zuwa garin Kauru, hedikwatar karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Ya koka da yadda al’ummomi a baya suka kwashe sa’o’i suna zagaye kogin Kaduna a yunkurinsu na mu’amala na kasuwanci da za su inganta zamantakewarsu da tattalin arzikinsu.
A yayin da yake kira ga ‘yan kwangilar da su tabbatar da cewa al’ummomin sun samu sana’o’in da ake bukata kuma sun tsunduma cikin aikin, dan majalisar ya kuma shawarci al’ummomin da su ba su goyon baya da hadin kan da ake bukata domin gudanar da aikin cikin nasara.
Mai ba da shawara kan aikin, Funso Facipe, ta ce ana sa ran kammala aikin gadar cikin watanni 13 masu zuwa.
A WANI LABARIN KUMA: Maikyau Ya Sha Rantsuwar Kama Aiki, A Matsayin Sabon Shugaban NBA
An rantsar da sabon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Yakubu Chonoko Maikyau a matsayin shugaban kungiyar na 31.
Daily Trust ta ruwiato cewa, An rantsar da Maikyau ne a wajen rufe taron shekara-shekara na kungiyar karo na 62 da aka gudanar a Eko Hotel, Victoria Island dake Legas a ranar jiya Juma’a.