Gwamnatin tarayya ta bai wa ‘yan wasan Najeriya da suka samu lambobin yabo a gasar kasashen Commonwealth da ke gudana a birnin Birmingham tare da masu horar da su tsabar kudi dalar Amurka 25,000.
Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Mista Sunday Dare a lokacin da yake gabatar da jawabin ga ‘yan wasa da masu horarwa a Hilton Garden, Birmingham a jiya, ya bayyana cewa wannan tukuicin na daya daga cikin shirye-shiryen da ma’aikatar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanya a gaba musamman don kara musu kwarin gwiwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Zamfara ta Yabawa Majalissar Dokokin Jihar Kan Amincewa Da Dokar Kare Hakkin Jama’a
Dare wanda ya samu wakilcin Darakta, Kungiyoyin FEAD da Chef De Mission, Dokta Simon Ebhojiaye, Dare ya bayyana cewa, ‘yan wasa da masu horar da ‘yan wasa suna samun karramawar ne saboda daukaka darajar kasarsu.
Ya ba da tabbacin ci gaba da jajircewar gwamnati wajen bunkasa wasanni a Najeriya. Wannan kuma ya ce, yana daya daga cikin dalilan kafa sashen wasannin motsa jiki a ma’aikatar don kara samar da damammaki ga nakasassu suma su jajirce da kuma yin fice a fagen wasanni.
Ministan ya bayyana kwarin gwiwar cewa tare da ‘yan wasa da masu horar da ‘yan wasa da jami’ai da kwararrun ma’aikatan Najeriya a Birmingham da irin jajircewarsu da kishin kasa, ko shakka babu kasar za ta iya samun karin bajinta a wasannin.
Ya bukace su da su ci gaba da mai da hankali da kuma kara jajircewa domin ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa cikin sahun kasashe na gaba a kwamitin wasanni.
Da take jawabi tun da farko, ‘yar wasan da ta samu lambar zinare mai nauyin kilo 59 na mata, Folashade Lawal, a madadin wadanda suka samu lambar yabo da masu horar da ‘yan wasa, sun nuna jin dadinsu kan yadda gwamnati ta himmatu, tare da bayar da tabbacin cewa kyautar za ta zaburar da ‘yan wasan wajen samun karin lambobin yabo ga kasar.
Ta danganta nasarorin da aka samu kawo yanzu ga daukakar Allah, aiki tare, da’a, aiki tukuru gami da tallafin da gwamnati ke bayarwa wajen bunkasa wasanni a kasar nan.
Olarinoye da Rafiatu Folashade Lawal, sun samu kyautar dala 5,000 kowanne, wanda ya samu lambar azurfa, Taiwo Laidi ya samu dala 3,000; ‘Yan wasan da suka samu lambar tagulla Edidiong Joseph Umaofia da Islamiyat Yusuf sun samu dala 2,000 yayin da kuma aka baiwa masu horar dasu dala 3,000 bi da bi.