Kasa da shekaru biyu kafin babban zaben na shekarar 2023, Gwamnatin Tarayya ta bukaci jam’iyyun siyasa da su kasan ce masu marawa mata baya domin su lashe wasu ofisoshi a babban zaben Mai zuwa.
Kazalika gwamnatin ta bukacu jam’iyyun siyasa, da su bar wasu ofisoshi na musamman, don mata su taka takara a zaben.
Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo SAN, ne ya yi wannan kiran, ya yin taron karawa juna sani na horas wa, kan bada shawarwari da sadar wa ga mata, da hadin gwiwar kungiyar mata ta Najeriya, wanda ya guda a jiya Alhamis a garin Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta Garkame Sakatariyar Yan jarida
Cibiyar Bincike da Ayyukan Ayyuka ta da tare da haɗin gwiwar Cibiyar Nazarin Ƙwadago ta Michael Imoudu a Ilorin da kuma Gidauniyar Bill da Melinda Gates ne su ka dauki dauyin Taron da ya guda na.
Kazalika Keyamo ya umarci masu ruwa da tsaki da su sanya matakan da za su karfafa kashi 49.32 na mahimmancin yawan al’ummar Najeriya, tare da ba da tabbacin ci gaban kasar baki daya.
Anashi bangaren Ko’dineton cibiyar Dr Yahaya Hashim ya ce, cibiyar ta horas da kungiyoyin farar hula sama da 500 tun daga shekarar 1994.
Comments 1