Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta kaddamar da ayyukan tarin bikin ‘kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata a Najeriya.
A cewar wata sanarwa a ranar Juma’a, Tallen ta ce tashe-tashen hankula da ambaliyar ruwa na baya-bayan nan sun kara yawan cin zarafin mata a kasar nan.
Gangamin ‘kwanaki 16 na fafutukar’ yunkuri ne na shekara-shekara na kasa da kasa da nufin magance matsalolin cin zarafin mata da ‘yan mata.
KU KARANTA KUMA An Tura Sojojin Najeriya Kasar Mali Domin Wanzar Da Zaman Lafiya
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Ana fara gangamin a kowace shekara a ranar 25 ga watan Nuwamba kuma za a shafe kwanaki 16 har zuwa ranar 10 ga Disamba, lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke bikin ranar kare hakkin ‘yancin dan Adam.
“Yau ne farkon kwanaki 16 na fafutukar yaki da cin zarafin mata. Najeriya ta bi sahun kasashen duniya don kaddamar da ayyukan tunawa a 2022 mai taken: ‘Hadewa! Yunkurin kawo karshen cin zarafin mata da ‘yan mata,” in ji Tallen.
“ Taken gangamin na 2022 ya ginu ne akan nauyin da ya rataya a wuyanmu na kawo karshen cin zarafin mata a kasar nan ko dai a matsayin abokan aikin yada labarai, masu tsara manufofi, daidaikun mutane, abokan ci gaba, kungiyoyin farar hula, ‘yan majalisa, har ma da mata da maza.
“Masu girma, ’yan uwa maza da mata, zan zama zakara a matsayin mai girma ministar harkokin mata yayin da muke shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati a shekarar 2023.
“Kididdigar da aka samu ta nuna cewa a Najeriya, kashi 30 cikin 100 na ‘yan mata da mata masu shekaru tsakanin 15 zuwa 49 an ruwaito sun fuskanci cin zarafi. Tashe-tashen hankula, rigingimun da suka dade, sabbin hanyoyin garkuwa da mutane da ambaliyar ruwa da ta mamaye duk fadin kasar sun kara dagula lamarin GBV.
A Wani Labarin Kuma An kaddamar da Gidan Ƴan Biafra a Amurka – Majiya
Kungiyar ‘yan kabilar Igbo a Amurka sun kaddamar da gidan Biafra a Oxon Hill, Maryland, Washington DC, Amurka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kungiyar ta ce an kafa gidan Biafra ne a makon da ya gabata “domin yiwa al’ummar Biafra hidima da kuma kawo ayyukan kasa da kasa ga mutane da kasashen da suke abokan Biafra.”