Gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin shawo kan yajin aikin ASUU, ASUP, ta fara biyan kuɗaɗen Ariyas
Gwamnatin Tarayya ta fara biyan kuɗaɗen Albashi, wanda Malaman Jami’o’i na Najeriya da Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya da Fasaha ke bin ta, a matsayin wani ƙoƙari na kawo ƙarshen yajin aikin Ƙungiyoyin.
Shugaban Ƙungiyar ASUP na Ƙasa Dr. Anderson Ezeibe da Shugaban Ƙungiyar ASUU na Jami’ar Minna Dr. Gbolahan Bolarin Suka tabbatar da haka, a jawaban su daban-daban a lokacin da aka zanta dasu a Abuja a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan taya murna ga Kowacce Jam’iyya taci zaɓen Shugaban Ƙasa a 2023 — Hadimar Buhari
Ƙungiyoyin guda biyu a halin yanzu suna cigaba da yin yajin aiki, biyo bayan kasawar Gwamnati na biyan haƙƙoƙin su da suka haɗa da ƙarin kuɗin Albashi, da Ƙuɗaɗen tafiyar da Makarantun da sauran su.
A yayin da ASUU ta fara yajin aikin ta a ranar 14 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022, ASUP a halin yanzu tana kan yajin aiki na gargaɗi na makonni biyu.
Dayake tabbatar da biyan kuɗaɗen a ranar Alhamis, Ezeibe yace wannan fari ne kawai.
Yace “Gwamnati ta fara maida hankali a kanmu. Sun fara biyan kuɗaɗen Albashi, kuɗaɗen Ariyas, abinda suka ƙi biya tunda farko.
Shima a nashi jawabin Bolarin yace “wasu daga cikin mambobin mu sun samu saƙo na biyan kuɗaɗen ƙarin Albashi, amma har yanzu ba’a turo masu Albashi ba.”
Comments 1