Gwamnatin tarayya ta ce ta himmatu wajen tabbatar da shata iyakokin Najeriya da Kamaru cikin inganci da daidaito.
Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a wurin taro karo na 34 na hukumar hadin kan Najeriya da Kamaru (NCMC) ranar Alhamis din nan a Abuja.
Kamfanin dillamcin labarai na Kasa NAN ya rawaito cewa, Hukumar kula da iyakokin kasa (NBC) ce ta shirya taron.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Malami ya ce a karkashin jagorancin Shugaban Hukumar, Mista Mahamat Saleh Annadif, NCMC ta samu ci gaba cikin sauri tare da samun nasarar aikin a cikin kankanin lokaci.
Ya ce atisayen gina ginshikan da aka kammala kwanan nan a cikin Lot 6A, B da C a cikin tsaunin Atlantika wani babban ci gaba ne bisa la’akari da wahalar shiga yankin.
“Har ila yau, yana cikin rahoton cewa a karkashin jagorancinku mai kyau, kun sami damar warware matsalolin da aka fuskanta a manyan wuraren da aka samu sabani, wanda aka rage daga 13 zuwa uku.
“Haka kuma a gare ku ne muka inganta yawan tarurrukan da muke yi. Wannan shi ne karo na biyu a cikin watanni tara.
“Ina so in yi godiya tare da nuna godiyarmu ga hukumomin da ke ba da gudummawa da jami’an tsaro kamar yadda suka yi iya kokarinsu.
“Na kuma fahimci cewa mun samu nasarar kammala aikin Lot 6 kuma yanzu haka mun shirya don Lot 7, kuma yana da kyau mu san cewa har yanzu muna da kudi don aiwatar da aikin Lot 7 daga Janairun 2023.
“Ina so in tabbatar muku da cewa Najeriya ta kuduri aniyar yin gaggawar aiwatar da wa’adin hukumar ta NCMC kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da kudirinta,” in ji Malami.
Karanta kuma: Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Wasu Sharuɗɗai Ga Masu Neman Mafaka Daga Kasar Kamaru
Ya yaba da kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kan wannan aiki, ya kuma bukaci da a yi la’akari da kyau ga abokan hadin gwiwa masu ba da gudummawa wajen aikin shata iyakar.
Malami ya kuma yi kira da a gaggauta warware sauran bangarorin guda uku da suka rage na rashin jituwa, inda ya kara da cewa shi da takwaransa na Kamaru za su hada kawunansu wuri guda domin saukaka kudurin.
Annadif ya ce taron na NCMC karo na 34 shaida ne ga kudurin hadin gwiwar kasashen biyu.
wanda aka nuna a cikin shekaru 20 da suka gabata don warware rikicin kan iyakar kasashen biyu cikin lumana.
“Wannan taro yana nuni ne da aniyar shugabannin tawagar biyu da na kasashen biyu na ganin an kai ga kammala aikin shata iyakar.
“An riga an kammala babban aiki a wannan bangaren Hukumar NCMC.
“Ina so in yi amfani da wannan damar in yaba wa dukkan jami’ai, wakilai, da kwararru daga Kamaru, Najeriya da Majalisar Dinkin Duniya bisa ayyukan da suka gudanar a wurare masu nisa da wahalar shiga.
“Na sake yabawa gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatin Kamaru bisa kokarin da suka yi na tabbatar da tsaron wadannan yankuna, wanda ya baiwa kungiyoyin da ke kan iyakokin kasar damar gudanar da ayyukansu tare da cimma wannan gagarumin sakamako,” in ji Annadif.
Jagoran tawagar Kamaru, Mista Zoah Michel, ya jinjinawa Malami da Annadif, inda ya kara da cewa kasarsa a shirye take kuma ta jajirce wajen gudanar da ayyukan NCMC.
Har ila yau, babban darakta na NBC, Mista Adamu Adaji ya nuna godiya ga tawagar daga Kamaru da Najeriya, da kuma masana.
Ya ce a cikin shekaru 20 da suka gabata hukumar NBC ta yi ta ratsa sama da kilomita 2100 na kan iyakar Najeriya da Kamaru.
“Wasu daga cikin mu sun biya mafi girman farashi na rasa rayukansu. Allah ya jikan su da rahama.
“Muna godiya ga gwamnatocin Najeriya da Kamaru bisa jajircewarsu da kokarinsu; da Majalisar Dinkin Duniya don ingantaccen aiki; da kuma abokan huldar mu,” in ji Adaji.
A wani labarin kuma: Daren yau da misalin karfe 8:45pm agogon Najeriya,Nijar, Kamaru da Chadi
Daren yau da misalin karfe 8:45pm agogon Najeriya,Nijar, Kamaru da Chadi, kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata karbi bakuncin Manchester United a gasar kofin FA na kasar Ingila. Ya kuke hasashen wasannin?