Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya (NRC), Fidet Okhiria, ya ce gwamnatin tarayya ta yi asarar kimanin Naira miliyan 113 sakamakon dakatar da zirga-zirgar jiragin kasan Kaduna zuwa Abuja.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa wannan ya faru ne sakamakon dakatar da zirga zirgar jirgin sama da watanni takwas.
KU KARANTA: Okowa, Tambuwal, Lamido Da Wasu Sun Gana Da Obasanjo A Abeokuta
Mista Okhiria ya ce wannan adadin kudin ya an samu asarar su ne ta hanyar amfani da takardar izinin shiga jirgin da akan siyar da ita ga masu son tafiya ta cikin sa, kuma an rasa samun kudin shiga tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
“Lokaci na ƙarshe da muka bincika, shine tsakanin watannin Fabrairu da Agusta. Mun yi asarar kusan Naira miliyan 113,” inji shi.
Sai dai ya ce ‘yan Najeriya da dama ma sun tafka asara a kaikaice sakamakon dakatar da ayyukan hanyar.
“Akwai mutane da suke sayarwa a cikin jirgin, akwai masu sayar da hajojin su a kusa da tashoshin, akwai kuma wadanda suka bude shaguna, kuma mutane suna ba su tallafi saboda jiragen suna aiki a baya.
Dangane da abinda za a tsammata yayin da jirgin Abuja — Kaduna ya ke shirin komawa aiki a ranar 5 ga Disamba, ya ce, “Tsarin da muke amfani da shi a baya har yanzu shi ne, kawai abin da ya bambanta fasinjojin shi ne sai fasinjojin sun nuna karin su ma shaidar zama yan Najeriya tukunnah.”
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kano Ta Fadi Lokacin Da Zata Kammala Tashar Lantarki Ta Dam ɗin Tiga
Kwamitin da gwamnatin Kano ta dorawa alhakin kula aikin inganta wutar lantarki a jihar ya tabbatar da cewa nan da wata guda za’a kammala aikin samar wutar megawat 7 da rabi don amfanin al’umma.
Mataimakin shugaban kwamitin Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi shine ya bada tabbacin a yammacin Asabar din nan, yayin da kwamitin karkashin jagorancin shugaban ma’aikata na jihar Kano kuma shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Usman Bala ya kai ziyarar duba aiki tashar wuta dake Dam din Tiga da gwamnatin Kano ke aikin samarwa.