Gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniya da Kungiyar ‘Yan Sanda ta Kasa da Kasa INTERPOL da Shirin Watsa Labarai na ‘Yan Sandan Afirka ta Yamma WAPIS domin kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.
Ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Dingyadi ne ya yi wannan maganar a ranar Talata yayin ganawa da kungiyar tsaro ta duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnoni Sun Gayyaci Gwamnan CBN don Ganawa Kan Sabbin Takardun Kudin Naira
Babban Daraktan hukumar ‘yan sanda ta INTERPOL, Kavanagh Stephen ya ziyarci hedikwatar ma’aikatar da ke Abuja.
Dingyadi ya sanar da cewa WAPIS da INTERPOL a shirye suke su marawa Najeriya baya domin ganin kasar ta samu zaman lafiya.
Ministan ya ce laifuka na da sarkakiya kuma sun bambanta daga wurare daban-daban, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su hada karfi da karfe domin kawo karshen kalubalen.
Dingyadi ya tabbatar da cewa a baya ana samun rashin hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro yayin da suke kin raba bayanai a tsakanin su.
“Muna da batutuwa da yawa na aikata laifuka. Muna bukatar hadin kai daga ko’ina da zai taimaka mana wajen dakile wadannan laifuka,” kamar yadda ya shaida wa Stephen.
Da yake jawabi, daraktan ya ce musayar bayanai tsakanin hukumomin tsaro, kan iyaka da na leken asiri zai haifar da sahihan bayanai da kuma na zamani.
“Ba mu zo nan don jin daɗi ba. Stephen ya kara da cewa, mun zo nan ne domin tabbatar da fahimtar yadda WAPIS za ta tallafa wa yammacin Afirka don raba bayanai tsakanin hukumomin tsaro yadda ya kamata.
A wani labarin kuma, Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan ‘Yan Sanda Da Na Sojoji Makonni Kafin Zuwan Zaben 2023
Hukumar hana fasa kwauri ta kasa NCS dake filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake jihar Legas ta kama miyagun kwayoyi da kayan sojoji da na ‘yan sanda.
An gano kayan ne a sashin kaya na Kamfanin Skyway Aviation Handling SAHCO, na reshen gida.