Gwamnatin tarayya za ta karkatar da ababen hawan dake bin babbar hanyar Legas zuwa Ibadan na tsawon kwanaki shida.
Kwamishinan ayyukan Gwamnatin tarayya dake Legas, Engr. Olukayode Popoola, a ranar Lahadi, ya sanar da karkatarwar, Wanda ya ce zai fara aiki daga ranar Litinin.
Ya ce an karkatar da ababen hawanne domin a hanzarta ayyukan gine-gine Tituna a yanki, yayin da gwamnati ke kokarin cimma burin da aka sa a gaba na kammala aikin.
Popoola ya bayyana cewa za a karkatar da ababen hawa ne a kan titin da ke kan hanyar Legas.
A cewar Popoola, sauyawa ababen hawan hanya zai baiwa kamfanin da ke gudanar da aikin wato Julius Berger damar gudanar da sashe na daya daga Shagamu zuwa Legas ya shimfida kwalta tsakanin Arepo zuwa Warewa, wanda ya kai tazarar kilomita daya da rabi.