Mazauna wasu kauyukan karamar hukumar Wase ta jihar Filato sun yi tir da yadda masu garkuwa da mutane ke yin shawagi a yankunan Sapiyo da Bangala na karamar hukumar, inda suka yi kira ga jami’an tsaro da su kawo musu dauki.
Mazauna kauyen sun kuma ce masu garkuwa da mutanen suna gudanar da ayyukansu ba dare ba Rana da bindigogi da sauran manyan makamai.
Shapi’i Sambo Haruna, wanda shi ne shugaban matasan garin Wase, ya shaida wa wakilin Jaridar Daily Trust cewa, a yau Larabar, hare-haren masu garkuwa da mutanen ya hana harkokin kasuwanci tare da jawo wahalhalu a yankunan da lamarin ya shafa.
“A halin yanzu masu garkuwa da mutane sun hana mazauna wurin gudanar da ayyukansu na yau da kullun, saboda haka jiya jami’an tsaro, ‘yan banga da sauran matasan Wase suka je wasu maboyarsu amma tuni Yan bindigan suka tsere.
“Muna zargin cewa suna da masu ba su bayanan sirri kan a wasu kauyukan dake kusa damu, da suke sanar da su dukkannin yunkurin mu.”
“Jami’an tsaro suna bakin kokarinsu amma duk da haka muna bukatar karin karfi don kawar da masu aikata laifuka a yankunan.
Shugaban matasan ya kara da cewa “Muna kuma kira ga matasa da kada su rika zagin kokarinmu domin idan ba a kula ba, matsalar za ta cinye kowa da kowa ciki har da wadanda ke zagin kokarinmu.”
Shapi’i ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da sauran al’ummar yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da zage damtse, wajen ganin an dakile duk wasu munanan ayyuka a karamar hukumar Wase domin jama’a su rika gudanar da ayyukansu na yau da kulun a yankunansu.