By Abbas Yakubu Yaura
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne da suka kai hari kauyen Rikwe-Chongu da ke gundumar Kwall a karamar hukumar Bassa a jihar Filato, sun kashe wani jami’in soji da wasu mutane biyu a daren ranar Alhamis.
Kakakin rundunar ta musamman na Operation Safe Haven (OPSH), Manjo Ishaku Takwa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis.
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Guterres Zai Ziyarci Najeriya Bayan Ya Kai Ziyara Rasha Da Ukraine
A cewar kakakin rundunar, tun daga lokacin ne aka tura sojoji zuwa cikin al’umma, saboda dawo da zaman lafiya.
Rahotanni sun ce jihar Filato na fama da hare-haren ‘yan bindiga a kowacce rana.
A farkon watan nan, an kashe akalla mutane 100 tare da kona gidaje tare da yin awon gaba da wasu da dama a wasu kauyuka goma da ke karamar hukumar Kanam ta jihar.
Takwa ya ce: “An kai hari da daddare a yankin a ranar 28 ga watan Afrilu; Dakarun mu da aka tura cikin al’umma sun dakile harin kuma ana cikin haka ne OPSH ta rasa soja guda. Wasu fararen hula biyu kuma sun mutu sakamakon harin.”
Sakataren yada labarai na kungiyar ci gaban Irigwe David Malison, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa an kashe mutanen yankin uku, mutum daya ya jikkata, an kuma kona gidaje da dama.
Comments 1