Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
A daidai lokacin da Ma’aikatar fina-finai ta kannywwod ta cika da fim na raye raye da Kuma nuna soyayya, sai ga shi kamfanin shirya fina-finai na Islamic Film Empire ya samar da wani fim Mai suna “Gari Guda” wanda Kuma ya da ce da koyarwar addinin Muslumci.
Fim din wanda aka shafe tsawon lokaci ana aikin sa, domin ganin an bi matakan da suka dace da koyarwar Muslumci, a yanzu an Kai ga kammala shi, Kuma nan gaba kadan za a sake shi a manyan Cinimu na Kasar nan, domin a kallo.
Kamar yadda mashiryin fim din Safyanu Lawal Kabo ya shaida Wa jaridar Dimukaradiyya cewa;
“Da ya ke a yanzu mutane sun saba da kallon fina-finai na Hausa a tsari na soyayya, sai muka ga akwai bukatar a sauya daga wannan sharing, zuwa shirya fim a Kan tsari na addinin Musulunci, domin fadakar da jama’a musamman wadanda ba musulmai ba, da su ke ganin Muslumci addini ne da ya ke koyar da ta’addanci.” Inji shi.
“Kuma wasu ma daga musulman, sun kasa gane hakikanin koyarwar Muslumcin, Don haka muka samar da wannan fim Mai suna “Gari Guda” Don bayar da ta mu gudummawar, Kuma Alhamdulillahi, a yanzu mun Kai ga kammala shi abin da ya rage a fara haska shi a Cinima. “a cewar shi.
Ganin cewar a yanzu babu kasuwar DVD ko ta wacce hanyar za ku bi don ganin fim din ya samu Isa ga Al’uma Baki daya?
“To lallai muna da hanyoyi da za mu bi wajen isar da shi ga masu kallo, duk yadda zamani ya zo Sai ka bi shi da haka, don haka mun yi kyakyawan tsarin da za mu yada shi, don sakon ya Isa, Kuma kudin da muka kashe ya dawo har mu ci ribar da za mu Kara yin wasu nan gaba, don manufar mu ba ta tsaya ga fim din “Gari Guda” ba kadai, mun fara ne za mu ci gaba da yi iya karfin mu”
Daga karshe ya yi fatan samun goyon bayan Jama’a Don ganin an samu nasarar da ake bukata wajen isar da sakon.