Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
Daya daga cikin jarumai masu tasiri a cikin fim din Labarana Abdullahi Amdaz, wanda aka fi sani da Excellency a cikin shirin, ya bayyana irin daga martabar shi da shirin ya yi da cewar, shi ne ya zame masa tsani, na samun dumbun masoya a duniya.
Abdullah Amdaz ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin jaridar Dimukaradiyya.
In da ya ke cewa”Duk da cewa ba wannan ba ne fim dina na farko da na yi, saboda na fi fina-finai masu yawa da wakokin Hausa da turanci da ka na Larabci, amma babu lokacin da na samu daukaka kamar lokacin da na fito a matsayin Excellency a cikin shirin Labarana, domin kuwa suna na ya daukaka a duniya, ba ma a nahiyar Afirka ba kadai, don haka ina godiya ga Allah da wannan matsayi da na samu. “Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana zargin Sojoji da kashe wani Direban Tasi har lahira da Duka
Ya Kara da cewa” Ita daukaka ta Allah ce, don haka ba mutum ba ne ya ke jawo ta, saboda tsawon lokacin da na yi ina harka waka, duk da na fi son waka a kan fim, ka ga ban samu daukaka ba a waka sai a fim, don haka duk abin da mutum zai yi a harkar sa ta rayuwa, to kawai ya nemi zabi a wajen Allah, don shi ne mai ba da nasara a duk lokacin da ya so” a cewar shi
“Don haka ina kira a jama’a su fahimci rayuwa, donmin komai na Allah ne, kuma yana bayar da shi ne a duk lokacin da ya so. “
Comments 1