By Abbas Yakubu Yaura
Fira Ministan Japan Fumio Kishida ya samu nasara a ranar litinin bayan daya jagoranci jam’iyyarsa mai mulki da gagarumin rinjaye a zabukan kasar daya gudana.
Kishida, mai sassaucin ra’ayi wanda ya kwashe wata guda yana kan karagar mulki, ya sha alwashin bunkasa tattalin arzikin kasa mafi girma na uku a duniya tare da sabon tsarin kashe kudi na annobar cutuka wanda yace zai tsara hakan a wannan watan.
Har ila yau, yace Japan za ta “ba da gudummawa wajen yin aiki don hana fitar da hayaki a Asiya”, kwana guda kafin ya nufi Glasgow don halartar taron COP26.
Jam’iyyar (LDP) wacce ata dade tana mulki tare da karamin abokin kawancenta Komeito sun lashe kujeru 293 daga cikin 465 na majalisar dokokin kasar, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka ruwaito yayin da aka kammala tattara sakamakon a hukumance.
“Zabe ne mai tsauri, amma mutane na nufin cewa suna son mu samar da makomar kasar a karkashin ingantacciyar gwamnatin LDP-Komeito da gwamnatin Kishida,” in ji Fira Minista.
“Mun samu kujeru 261 masu daraja ga jam’iyyar LDP. A matsayinmu na jam’iyya mai alhakin son cika umarnin jama’a.”
Masu saka hannun jari sun yi murna da sakamakon, tare da ma’aunin hannun jari na Nikkei inda ya karu da sama da kashi biyu cikin dari bayan da jam’iyar dake mulki ta takaita asarar data yi don doke hasashen fitar da gwani.A baya dai kawancen ya rike kujeru 305 a majalisar dokokin kasar, sannan kuma jam’iyyar LDP tana da kujeru 276 ita kadai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaban mai shekaru 64 da haifuwa ya bayyana shirye-shiryen magance rashin daidaito da manufofin kasuwanci na magabatansa Yoshihide Suga da Shinzo Abe, firaministan kasar Japan mafi dadewa a kan karagar mulki.Jam’iyyar LDP ta kuma yi alkawarin kara yawan kudaden da ake kashewa a fannin tsaro domin tinkarar barazana daga kasar Sin, da Koriya ta Arewa.
Kafofin yada labaran kasar Japan sun ce kimanin kashi 56 cikin dari na masu kada kuri’a ne suka kada kuri’unsu, kasa da karancin fitowar jama’a da suka dabaibaye zabukan kasar a ‘yan shekarun nan.