Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya kamu da cutar Corana ta COVID-19 kwanaki biyo bayan an feshe shi da allura rigafin cutar kamar yadda ofsihin sa ya bayyana a yau asabar.
Wannan gwaji nashi ya na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke tirka-tirkar yadda za ta dakile sake bullowar cutar karo na uku inda ta hallaka mutane sama da dubu sha uku daga cikin mutane dubu dari shida da ashirin da suka harbu da cuta.
A ranar Alhamis ne dai aka gwangwanje Firai Ministan da allurar rigafin COVID-19 samfurin Sinoporham na kasar Sin wanda da ma tuni ta baiwa Pakistan allurar kimanin miliyan guda.
Kasar dai mai yawan al’umma miliyan dari biyu da ashirin na daga cikin kasashen da suka yi biris da dokar kulle, duk da kasancewar makotan ta sun ayyana hakan..