By Abbas Yakubu yaura
Firaministan Habasha Abiy Ahmed a ranar Talata ya bukaci ‘yan tawayen Tigray dasu mika wuya, sannan yana mai ikirarin cewa dakarun gwamnati na dab da samun nasara mako guda kacal bayan ya sha alwashin jagorantar ayyukan soji a fagen daga.
Abiy, wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel na shekarar 2019, a wani tsokaci da aka watsa a kafafen yada labarai na kasar yace, ” matasan Tigray suna halaka kamar ganyaye, sanin cewa an kayar da su, wanda ba shi da kyakkyawar manufa ko shiri ne ke jagorantar su.”
Sannan yace “Ya kamata ‘yan tawayen Tigray su mika wuya a yau ga rundunar tsaron kasar Habasha, ga runduna ta musamman, ga mayakan sa kai da kuma jama’a.”
Sai dai Hotunan na ranar Talata shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin faifan bidiyo dake nuna Abiy, sanye da kakin sojoji, a wani abin daya bayyana a yankin Afar dake arewa maso gabashin kasar.
Yankin dai ya kasance wurin da aka gwabza kazamin fada a ‘yan makonnin da suka gabata a daidai lokacin da kungiyar ‘yan tawayen Tigray TPLF ke kokarin kwace iko da wata babbar hanya da ke kaiwa Addis Ababa babban birnin kasar.
A ranar Lahadin data gabata ne kafafen yada labaran kasar suka yi ikirarin cewa sojojin kasar ne ke iko da garin Chifra na karamar hukumar Afar, kuma Abiy yace a ranar Talata irin wadannan nasarorin za su koma yamma, a yankin Amhara.
“An ci galaba a kan makiya, mun samu nasarar da ba za a yi tsammani ba tare da rundunar sojojin gabas a rana guda Yanzu a yankin yamma, za mu sake maimaita wannan nasara,” in ji shi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanarwar da aka fitar a makon da ya gabata na cewa Abiy, tsohon Laftanar-Kanar a soji, zai nufi fagen fama, ya zo ne bayan da kungiyar TPLF ta yi ikirarin cewa tana iko da garin Shewa Robit, a wani gari mai tazarar kilomita 220 daga arewa maso gabashin Addis Ababa.