Nuno Gomes Nabiam, Firaministan Guinea-Bissau, da wasu ministocinsa uku, gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.
An killace su a wani hotel da Bissau babban birnin kasar bayan tabbatar da sakamakon gwajin a ranar Talata, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar.
Yanzu sama da mutum 70 suka kamu da cutar a kasar da ke yammacin Afirka, yayin da mutum guda ya mutu.
Ministan lafiya na kasar Antonio Deuna ya yi gargadin cewa adadin na iya karuwa kamar yadda rahoton Bbc Hausa ya tabbatar.